Chuck Hagel ya kare musayar fursuna

Chuck Hagel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chuck Hagel

Sakataren tsaron Amirka, Chuck Hagel, ya kare matakin da ya dauka na sakin 'yan Taliban 5 daga sansanin Guantanamo, a madadin wani sojan Amirkan da 'yan Taliban din suka saki.

Ana dai zargin mista Hagel da kin sanar da majalisar dokokin Amirka tukuna, kafin ya yanke shawarar.

To amma in ji Chuck Hagel din, dole ta sa jami'ai suka dauki matakin gaggawa, saboda sun yi amunnar rayuwar sojan - watau Sergeant Bowe Bergdhal - tana cikin hadari.

A Afghanistan ne aka kama sojan Amirkan kusan shekaru biyar kenan, kuma jiya ne aka sako shi.

Mista Hagel ya ce, bai san ko wannan musayar zata sa a sami cigaba wajen sasantawa da 'yan Taliban ba.

Amma ya ce yana fatan hakan ya faru.