An nemi dakatar da hukuncin kisa a Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption MDD tace kasar Iran ita ce a sahub gaba wajen yankewa mutane hukuncin kisa.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta bukaci Iran da kar ta zartar da hukuncin kisa ga dan Siyasar nan da ya fandare wato Gholamreza Khosravi Savajani bayan da aka sanar da 'yan uwansa cewa za a rataye shi a yau lahadi.

An dai yanke masa hukuncin kisa ne shekaru hudu da suka gabata, da ake zarginsa da alaka da kungiyar 'yan tawaye da suke kokarin hambarar da gwamnatin Iran.

Bafaranshen nan kuma mazaunin Iran dan kungiyar adawa ta The Peoples Mujahideen yace ba bu adalci a hukuncin da aka yanke masa ba.

Itama MDD ta ce kasar Iran ita ce a sahun gaba-gaba wajen yankewa mutane hukuncin kisa a duniya, kuma adadin wadanda ake yankewa hukuncin ya hauhawa tun shekarar da ta gabata bayan zaben shugaba Hassan Rouhani.