An girke dakarun tsaro a Thailand

Shugaban Thailand Janal Prayuth Chan-o-cha Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Janal Chan-o-cha shi ya jagoranci juyin mulki a kasar a watan da ya gabata.

An girke dubban jami'an Soji da 'yan sanda a babban birnin kasar Thailand Bangkok,domin dakile barazanar masu zanga-zangar kin goyon bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan da ya gabata.

An rufe wasu daga cikin tashoshin jiragen kasa da manyan shaguna a Bangkok gabannin zanga-zangar da aka shirya.

Wakilin BBC a Bangkok yace kusan jama'a sun kauracewa yankin da ake hada-hadar kasuwanci a birnin, bayan da sojoji sun killace shi.

A ranar juma'a da ta gabata ne shugaban kasar Thailand na yanzu Janal Prayuth Chan-oCha ya bukaci dukkan bangarorin dake zanga-zanga a kasar da su dakatar da yin haka domin a samu cimma sasantawar da ake kokarin yi dan samun daidaito a siyasar Thailand.

Haka kuma Janal Chan-o-cha ya kara da cewar ba ya tsammanin za a gudanar da zabe a kasar nan da shekara guda.