Za a je kotu kan 'yan matan Chibok

Bring back our girls Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Kungiyar Bring back our girls ta zargi gwamnati da yin katsalandan cikin al'amuranta

Masu zanga-zanga a Abuja, babban birnin Nigeria kan matsa lamba ga gwamnatin kasar ta ceto 'yan matan Chibok sun ce za su je kotu saboda matakin da 'yan sandan birnin suka dauka na hana su gangami.

Ranar Litnin ne dai rundunar 'yan sandan Abuja ta haramta dukkan tarukan da suka shafi fafutika ta ceto 'yan matan sakandaren Chibok wadda kungiyar nan ta Bring Back Our Girls, wato a maido mana 'yan matanmu ke sahun gaba-gaba.

Rundunar dai ta ce tarurrukan da ake yi babbar barazana ce ga tsaron kasa.

Sai dai masu zanga-zangar sun ce kundin tsarin mulkin kasar ya ba su damar yin gangami na zaman lafiya, don haka ba su ga dalilin da zai sa a hana su ba.

A cewarsu kotu ce kawai ke da hurumin hana su zanga-zangar.