'Yan Nigeria na tserewa zuwa Kamaru

Hakkin mallakar hoto NEMA

'Yan Nigeria da dama ne daga garin Kala Balge cikin jihar Borno ke tserewa daga gidajensu zuwa jamhuriyar Kamaru saboda karuwar hare-hare.

Daruruwan mutane ne ciki har da Mata da kananan yara suna can a kan iyakar Kamaru sun rasa abin yi ba tare da abinci, ruwan sha ko wani agaji ba.

Ko da yake Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya ta ce tana fatan kai wa mutanen dauki da zarar ta samu hanyar kai sufuri, sai dai mutanen yankin sun yi korafin cewa an yi biris da halin da suke ciki.

Rahotanni sun ce ba wannan ne karon farko da mutane daga jihohin arewa maso gabashin Nijeriya ke yin gudun hijira zuwa kasashe makwabta ba, don tsira daga hare-haren Kungiyar Boko Haram

Karin bayani