'Yan bindiga sun kashe mutane 16 a Mubi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna garin sun ce ba su taba ganin tashin hankali kamar na harin da aka kai ba.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa da ke Nigeria ta ce harin bam din da aka kai a garin Mubi ranar Lahadi ya hallaka akalla mutane 16 tare da jikkata wasu da daama.

Kakakin rundunar, Usman Abubakar, ya shaidawa BBC cewa wurin da aka kai harin wata Mashaya ce da mutane suke kallon kwallo a talabijin.

Mazauna garin na Mubi sun ce ba su taba ganin tashin hankali irin na ranar ta Lahadi ba.

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kama mutum daya wanda take zargi da hannu a harin na garin Mubi.

Kakakin rundunar, Chris Olukolade, yace suna nan sun gudanar da bincike kan lamarin.

Garin -- wanda ke kan iyaka da kasar Kamaru -- yana cikin jihar Adamawa ne - daya daga cikikn jihohi uku da aka kafa ma dokar ta-baci sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa.

Kungiyar dai ta kai hare-hare da dama a yankin cikin watan Maris inda ta hallaka akalla mutane dari biyu.

Karin bayani