Likitoci sun fara yajin aiki a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Likitocin na Nigeria sun ce za su ci gaba da yajin aiki.

Kungiyar likitoci da ke aiki a karkashin gwamnatin tarayyar Nigeria sun fara yajin gargadi na kwanaki uku saboda matakin da gwamnati ta dauka na kin kyautata albashinsu.

Likitocin sun ce gwamnatin ta dauki alkawarin kara musu albashi a shekarar 2013 amma ta ki cika alkawarin.

A cewar kungiyar hakan ne ya tilasta musu fara yajin aikin na kwanaki uku domin jan hankalin gwamnati ta biya bukatunsu.

Kungiyar likitocin ta Nigeria ta ce za ta gudanar da yajin aiki na sai-illa-masha-Allahu idan bayan kwanaki uku gwamnati ba ta cika musu alwarin ba.

Karin bayani