Sabuwar gwamnatin hadin kan Palasdinawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabuwar gwamnatin matakin farko ne na kawo karshen rashin jituwa tsakanin Fatah da Hamas

An rantsar da sabuwar gwamnatin hadin kan Paladinawa a birnin Ramallah.

Kafa sabuwar gwamnatin shi ne matakin farko na kawo karshen rashin jituwa tsakanin kungiyoyin Palasdinawa na Hamas da Fatah wadanda suka dade ba sa ga-miciji da juna.

A cikin shekaru 7 da shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas, ya kwashe yana mulki kungiyar Fatah ce ke gabar yammacin kogin Jordan, yayin da kungiyar Hamas ke jan ragamar yankin Gaza.

Sasantawar da suka yi za ta ba da dama a gudanar da sabon zabe nan da watanni shida.

Sai dai Pirai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bukaci shugabannin duniya da kada su amince da duk wata sabuwar gwamnati da za ta hada da kungiyar Hamas.

Karin bayani