Annobar cutar MERS a Saudiyya

kwayar cutar MERS mai saurin kisa
Image caption kwayar cutar MERS mai saurin kisa

A kasar Saudiyya an hukumomi sun bayyana gagarumar karuwar yawan mutanen da cutar nan mai saurin kisa mai suna MERS ta hallaka a kasar.

Jami'an kiwon lafiya sun ce, ya zuwa yanzu cutar dake zuwa da tsananin mura da zazzabi mai zafi ta hallaka mutane dari biyu da tamanin da biyu.

Kuma an bayyana cewar, wasu mutanen dari da goma sha uku sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya.

Batun wannan cuta dai ya zama wata badakala a Saudiyya inda koda a yau an sallami mataimakin kiwon lafiya na kasar.

Karin bayani