An hana sakonnin wayar salula a CAR

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rubuta sakonin ta wayar salula

Hukumomi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun dakatar da musayar sakonni a rubuce ta wayar salula na dan wani lokaci.

Hukumomin kasar sun ce, an dauki wannan mataki ne domin daidaita al'amuran tsaro a kasar da ta dauki lokaci tana fama da rikicin addini.

An dai dauki matakin dakatar da musayar sakonnin ne bayan an shafe makonni ana mummunar zanga-zanga da kuma kiran a yi yajin aiki.

Rahotanni sun ce an shirya zanga-zangar ce ta hanyar amfani da sakonnin wayar salula.