Obama ya gargadi Rasha game da kafa daula

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama na ziyarsa ta farko ne a Poland

Shugaba Obama ya gargadi Rasha game da abin da ya kira take-takenta na manakisa a kasar Ukraine.

A jawabin da yayi a Warsaw, shugaba Obama ya ce, zamanin kafa wata babbar daula ya wuce, kuma yanzu ba lokaci ba ne da manyan kasashe za su ci zalin kananan kasashe.

"Na zo birnin Warsaw a madadin Amurka, kuma a madadin kungiyar tsaro ta NATO, domin jaddada aniyarmu ta tabbatar da tsaron kasar Poland."

A ranar Talata ne shugaba Obama ya sanar da wani shirin karfafa sojin Amurka a kasashen gabashin Turai da zai lashe dala biliyan daya.