Boko Haram: Ana zaman dar-dar a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Haka kuma fashe-fashen sun tilasta wa daliban barin makarantar a garin na Fotokol.

Rahotanni daga garin Fotokol na Kamaru na cewa malaman makaranta na zaman dar-dar saboda harin da ake zargin 'yan Boko Haram da kai wa a Borno da ke Nigeria.

Mazauna garin Fotokol da ke bakin iyakar Kamaru da Najeriya sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa daga garin Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

Hakan dai, a cewarsu, ya jefa su cikin zaman dara-dar, musamman malaman makarantar boko, inda wasunsu suka yi kaura daga garin.

Haka kuma fashe-fashen sun tilasta wa daliban barin makarantar a garin na Fotokol.

Karin bayani