An kame wadanda suka 'sace' 'yan China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Kamaru sun kame wasu mutane shida da ake zargin su da sace wasu 'yan kasar China su goma a garin Waza dake lardin arewa na kasar.

Rahotanni sun ce uku daga cikin mutanen da aka kame 'yan Najeriya ne wadanda ake zarginsu da garkuwa da 'yan kasar Chinan fiye da makonni biyu da suka gabata.

Hukumomi a Kamarun dai sun daura alhakin sace mutanen ne kan 'yan kungiyar Boko Haram wadanda ke kai hare hare a wasu yankuna dake kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Kamaru.

A karshen makon daya gabata ne aka sako wasu 'yan kasar Italiya biyu tare da wani dan kasar Canada bayan da suka shafe fiye da watanni biyu a hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka yi garkuwa da su.