An hana bukin tunawa da Tiananmen a China

Zanga Zanga a dandalin Tiananmen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga Zanga a dandalin Tiananmen

Hukumomi a kasar China sun karfafa matakan tsaron da suka dauka domin hana duk wasu bukukuwa na tunawa da ranar da aka tarwatsa wata zanga-zanga da aka yi a dandalin Tiananmen yau shekaru 25 cif da suka gabata.

Babu wani wanda aka kyale ya yi bukin tunawa da ranar ko tattaunawa game da ranar ko kuma bayar da rahoton lamarin inda daruruwa ko ma dubban mutane suka rasa rayukkansu.

A 'yan makonnin nan an kame masu fafutuka da dama da masu sukar lamirin gwamnati da lauyoyi an kuma yi ma kafofin watsa labarai na kasashen waje kashedin mummunan sakamakon da zai biyo bayan ba da labarin batun, yayinda kuma aka dauki matakai na hana mutane amfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

Karin bayani