Niger: Kotu ta ce a cigaba da tsare 'yan adawa

Jami'an gidan yarin birnin Yamai Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an gidan yarin birnin Yamai Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar wata babbar kotu a Yamai ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu shugabannin jam'iyyar Moden Lumana mai adawa.

Lauyan Jam'iyar ta Moden Lumana ya ce alkalin gwamnati mai shigar da kara, na zargin mutanen da yake karewa su 35 'yan jam'iyar Moden Liumana da laifin yiwa kasa zagon kasa.

A cikin wasu tsauraran matakan tsaro aka kai jami'an jam'iyar ta Moden Lumana kotu, yayinda aka hana magoya bayansu da 'yan jarida shiga.

'Yan sanda sun cafke su ne bayan hare-haren da wasu mutane dauke da makamai suka kai gidan mataimakin shugaban majalisar dokoki Ben umar Mohammed, da wanda aka kai cibiyar jam'iyar PNDS Tarayya.