'Yan bindiga sun kai hari a Madagali

'Yan kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Rahotanni sun ce maharan sun kwashe makamai da kuma wasu motocin soji biyu da ke garin.

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Madagali dake jihar Adamawa.

Maharan sun hallaka mutane biyu tare da kona sakatariyar karamar hukumar da kuma wani coci da ke garin.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa maharan sun kai harin ne a ranar alhamis inda suka shafe fiye da sa'o'i uku suna ba ta kashi da sojojin da ke samar da tsaro a garin.

Sai dai rahotanni sun ce bayan maharan sun fice ne wani jirgin saman soji ya yi ta shawagi a garin inda ya jefa bama bamai har guda uku wadanda suka yi sanadiyar mutuwar karin wasu mutane uku.

Karin bayani