Za a yi taro kan Boko Haram a Burtaniya

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Heague
Image caption Taron na London ci gaba ne na taron da aka yi a Paris a ranar 17 ga watan Mayu kan magance ayyukan Boko Haram

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague, zai karbi bakuncin taron ministoci kan matsalar tsaro a arewacin Nigeria a ranar Alhamis mai zuwa.

Taron wani bangare ne na taron koli na duniya kan magance matsalar fyade a wuraren da ake samun tashe-tashen hankula.

Wannan taron da za a yi London ya biyo bayan taron kolin da aka yi a Paris kan Boko Haram a ranar 17 ga watan Mayu.

Wakilan ma'aikatar wajen Najeriya da na Benin da Chadi da Kamaru da Nijar da Burtaniya da Amurka, Faransa, Canada da kuma tarayyar Turai ne za su halarci taron, domin ci gaba da tsara hanyoyin da za su magance matsalar Boko Haram.

Mr. Hague ya ce, "Hakan na nuna jajircewar kasashen da ke yankin tare da taimakon kasashen duniya, na ganin an samu galaba a kan Boko Haram a Najeriya. Hakan kuma zai taimaka wajen sakin 'yan mata 'yan makarantar da aka sace."

Ana shirye-shiryen wannan taron ne a daidai lokacin da wata cibiyar lura da 'yan gudun hijira ta kasar Norway mai cibiya a Switzerland ta fitar da wani rahoto inda ta ce 'yan Boko Haram sun kashe mutane akalla 3,300 a wannan shekarar.

Rahoton ya ce gwamnatin Nigeria ta yi kasa a gwiwa a kokarin kawo karshen zubar da jini sakamakon ayyukan 'yan Boko Haram.