Sabon shugaban CBN ya gabatar da manufofinsa

Ginin Babban bankin Nigeria, CBN
Bayanan hoto,

Jim kadan da gabatar da manufofin Mr. Emefiele ne darajar naira ta fadi a kasuwar hada-hadar kudi ta kasar

Sabon shugaban babban bankin Nigeria CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana manufofinsa dangane da tattalin arzikin kasar.

Mista Emefeile ya ce sannu a hankali zai rage kudin ruwa domin 'yan kasuwa su samu damar zuba jari cikin sauki a kasar.

Haka kuma ya dakatar da kudin da bakuna ke karba daga wajen mutane, idan sun yi hada-hadar kudi fiye da naira dubu 500, a karkashin tsarin rage amfani da takardun kudi na kasar.

Sabon shugaban na CBN ya ce zai gabatar da wani sabon tsari kan yadda za a samar wa kananan kamfanoni tallafi domin rage talauci a kasar.