G7 za ta garkamawa Rasha karin takunkumi

Taron koli na kungiyar G7 a Brussels Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron koli na kungiyar G7 a Brussels

Shugabannin kasashen yammacin duniya dake ganawa a Brussels sun ce a shirye suke su garkama wa Rasha karin wani takunkumi idan har ta cigaba da wargaza gabashin Ukraine.

Wata sanarwa ta hadin-gwiwa da Shugabannin kasashen na kungiyar G7 suka bayar, ta ce ba a amince da matakan da Rasha ke dauka ba, kuma lallai ne ta daina.

Taron Kolin shine na farko tun bayan da aka kori Rashar daga kungiyar sakamakon mamayar da ta yi ma yankin Crimea.

Ta zo ne a daidai lokacinda ake cigaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da 'yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukraine.

Kasar ta Rasha dai ta musanta cewar tana da hannu a tashe-tashen hankulan na Ukraine.

Karin bayani