Amirka za ta gina kurkuku a Nijar

Tutar Amirka Hakkin mallakar hoto
Image caption Tutar Amirka

Ofishin jakadancin Amirka a Nijar ya tabbatar da Amirkar za ta tallafa ma gwamnatin Nijar wajen gina wani sabon gidan yari irin na zamani a Yamai, babban birnin kasar.

Sai dai ofishin bai yi wani karin haske ba dangane da ranar da za a fara ayyukan.

Ma'aikatar ministan shari'a ta Nijar din dai ba ta tabbatar da labarin ba.

Ta ce ba ta da masaniya a kan lamarin.

Maganar gina sabon gidan kurkuku irin na zamani a Yamai ta biyo bayan harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai wa gidan yarin birnin a watan Yunin 2013.

A lokacin harin wasu da ake zargi da ayyukan ta'addanci da ke daure sun tsere, amma an samu an kamo wasunsu.