Syria- An sake zaben shugaba Assad

Zaben shugaban kasar Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaben shugaban kasar Syria

Hukumomi a kasar Syria sun ce an sake zaben Shugaba Bashar Hafeez al- Assad da kusan kashi tamanin da tara na kuri'un da aka kada.

Shugaban majalisar dokokin Syriar Mohammed al-Laham ne ya ba da sanarwar sakamakon zaben da cewa Mr Assad ya samu lashe zaben a matsayin Shugaban kasar da mafi rinjayen kuri'un da aka kada.

An gudanar da zaben ne a daidai lokacinda ake gwabza yakin basasa, kuma mutanen dake karkashin yankunan da gwamnati ke iko da su ne kawai suka yi zaben.

'Yan adawa na Syriar sun kaurace masa suna cewar wani shiri ne kawai, to amma gwamnati ta ce yawan mutanen da suka kaada kuri'un na su, sun kai kashi saba'in da ukku bisa dari.

Magoya bayan Mr Assad a birnin Damascus, suna shagulgulan samun nasara.