Ana ci gaba da mika ta'aziyyar Sarkin Kano

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sarkin ya mutu bayan doguwar jiya yana da shekaru 84 a duniya

Yayin da masarautar Kano ta shiga makokin Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ana ci gaba da samun sakonnin ta'aziyyar mutuwarsa.

Hamshakin attajirin nan da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka kuma wanda ya fito daga jihar Kanon, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana alhininsa game da rasuwar a shafinsa na Twitter.

Tsohon shugaban mulkin Soji a Najeriya yana cikin manyan mutanen da suka je Kano domin halartar jana'izar marigayin kuma ya bayyana Sarkin Kanon da cewa mutum ne mai kishin jama'arsa ne.

"Hakika wannan rashin an yi mana a lokacin da jihar Kano da kuma kasarmu Najeriya ke bukatar dattaku na sanin ya kamata kamar na marigayi Dr. Ado Bayero."

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya mika ta'aziyyarsa, inda yake bayyana Sarkin da cewa mutum ne mai gaskiya da son hadin kan al'umma tare da kaunar zaman lafiya.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayana alhininsa game da rasuwar sarkin Kano, inda ya ce mutum ne mai kwatanta adalci da fadin gaskiya kuma yana son ilimi.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta fitar da sanarwar ta'aziyya, tana mai cewa mutuwarsa lamari ne da ya kada ta, kuma kasar da ma duniya sun yi rashin gwarzon basarake.