Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya rasu

Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarkin na Kano ya shafe lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya.

Rahotannin da muke samu daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cewa Allah yayi wa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa.

Sarkin Kano wanda ya hau kujerar mulki tun a shekarar 1963, ya rasu ne sakamakon doguwar jinya.

Dan shekaru 84, Margayi Alhaji Ado Bayero, shi ne Sarkin da ya fi kowanne dadewa a kan mulki a tarihin masarautar Kano.

Ya shafe shekaru 51 a kan karagar mulki.

Alhaji Ado Bayero tsohon ma'aikacin banki ne kuma ya yi aikin dan sanda.

Ya kuma taba zama dan majalisar dokoki sannan kuma tsohon jami'in diplomasiya.

Za a yi jana'izar sa bayan sallar Juma'a a Kano.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani a wannan shafin.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masarautar Kano na dasawa da masauratar Birtaniya. Sarkin Kano tare da Yarima Charles