Ranar tunawa da sojojin taron-dangi

Wani tsohon soja da ya kai ziyara makabartar da aka binne tsaffin sojojin da suka mutu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban sojoji ne dai suka rasa rayukansu, a kokarin kwace lardin Normandy daga hannun sojojin Hitler a shekarar 1944

An kai koluluwar bukukuwan cika shekaru saba'in a jibge sojojin taron-dangi mafi girma a tarihin duniya a arewacin kasar Faransa.

Bukukuwan sun soma na da tsakar daren nan a gadar Pegasus,wanda ya yi daidai lokaci irin wannan da sojojin taron dangin kasashen duniya suka kaddamar da wani harin sojin ruwa mafi girma a duniya.

Nan gaba ne shugaban Faransa Francoise Hollande da shugaba Obama da sarauniya Elizabeth tare da sauran shugabannin kasashen duniya da daruruwan tsaffin sojoji, za su yi jinjinar girmamawa ga dubban Sojojin kasa da na Ruwa da na Sama wadanda suka mutu, wajen kwato tsuburin Normandy daga hannun sojojin Hitler a watan Yunin shekarar alif dari tara da arba'in da hudu.

A jiya Alhamis ne tsaffin sojojin tare da yarima mai jiran gadin masarautar Burtaniya Yarima Charles suka kai ziyarar ban girma makabartar da aka binne tsaffin sojojin da suka taka muhimmiyar rawa wajen kwato lardin na Normandy.