Gombe ta musanta kai mata harin bam

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption jihar Gombe dai na makwabtaka da jihar Borno inda mayakan Boko Haram ke kai hare-hare kusan kullum.

Jami'ai a fadar gwamnatin jihar Gombe da ke arewa maso yammacin Najeriya sun nisanta tashin da wasu abubuwa masu fashewa suka yi a cikin wata motar jami'an tsaron fadar daga kasancewa harin bom.

Da marecen ranar Alhamis ne dai aka samu fashewar ababen a cikin motar wadda ke ajiye bakin kofar shiga fadar gwamnatin, abin da wasu rahotannin da hukumomi ba su tabbatar ba ke cewa yayi sanadiyar mutuwar mutane uku.

''kafin ka shiga gidan gwamna akwai wani tanki mai sulke na soja; duk abin da ya faru ba hari ba ne daga ita wannan motar ne'' inji shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Alhaji Ahmad Yayari.

Mazauna birnin na Gombe dai sun ce an ji karar fashewar a ko'ina a garin abin da ya jefa tsoro da firgita a zukatan jama'a.

Karin bayani