An nada sabon sarki a masarautar Gombe

Tsosho sarkin Gombe,  Alhaji Shehu Usman Abubakar Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Mahaifin sabon sarkin, Alhaji Shehu Usman Abubakar ya rasu a wani asibiti a birnin London

An nada Abubakar Shehu Abubakar, a matsayin sabon sarkin Gombe, kuma ya gaji mahaifinsa marigayi Alhaji Shehu Usman Abubakar, wanda Allah yayi wa rasuwa a makon jiya.

An nada sabon sarkin na Masarautar Gombe ne a ranar Juma'a.

Kafin zabe da nadin sabon sarkin, gwamnatin jihar Gombe ta yi garambawul ga Majalisar zaben sarkin tare da sauya dokar zaben sarki ta shekarar 2004.

Majalisar masu zaben sarkin kuma ta mika wa gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo sunayen mutane uku shi kuma ya amince da mutum guda a matsayin sabon sarkin.

Sabon sarkin mai kimanin shekaru 37 da haihuwa, yanzu ya zama sarkin Gombe na goma sha daya.

Bayanan tarihinsa sun nuna cewa ya yi karatun digiri a fannin kimiyar Siyasa a Jami'ar Maiduguri ya kammala a 2005, kana ya zamo kansila a karamar hukumar Gombe, kuma kafin nadinsa shi ne San-Turakin Gombe.

Karin bayani