Jonathan ya kadu da rasuwar Sarkin Kano

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Jonathan da Margayi Alhaji Ado Bayero

Shugaban Nigeria, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana matukar kaduwa game da rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, Mr Jonathan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Nigeria baki daya.

Mr Jonathan ya mika ta'aziyarsa ga iyalan sarkin da kuma al'ummar Kano a madadin gwamnatin tarayya da kuma 'yan Nigeria.

Shugaban kasar ya ce za a tuna da Alhaji Ado Bayero a matsayin mai son zaman lafiya wanda ya kulla dankon zumuncin da al'ummomi daban-daban a kasar.

Shugaba Jonathan ya ce Sarkin Kano na daga cikin mutanen da yake girmamawa a Nigeria wanda ke daukaka martabar sarautar gargajiya.