Cin zarafin mata babban laifi ne a Masar

Shugaban rikon kwarya na Masar Adly Mansour Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukuncin shekaru 5 a gidan kaso ne ya rataya akan duk wanda aka samu da cin rafin mata.

A karon farko gwamnatin kasar Masar ta ayyana cin zarafin mata a matsayin babban laifi.

Dokar zata hukunta Mazan da suka ci zarafin mata a bayyanar jama'a da za man gidan kaso na fiye da shekaru biyar.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar da ta gabata, ya gano cewa kusan dukkan matan Masar sun fuskanci cin zarafi daga maza, wala'allah ta hanyar yi musu dan kira, ko kuma yin fito idan sun zo wucewa, ko ma yi musu fyade dungurugum.

Tun bayan juyin juya halin da ya hambarar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011 ake samun yawaitar cin zarafin mata a kasar, ciki kuwa har da yi wa mata fyade a tsakiyar jama'a inda ake yin zanga-zangar yiwa gwamnati bore.

A iya cewa wannan doka na daga cikin ayyuka na karshe da shugaban Masar na Rikon kwarya Adly Mansour ya ayyana gabannin saukarsa daga mukami.