Za a bayyana sabon Sarkin Kano Lahadi

Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso
Image caption Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso

Rahotanni daga Kano na cewa gwamnatin jihar ta ce ranar Lahadi zata bayyana sunan sabon Sarkin Kano.

Sabon Sarkin shi ne zai gaji Marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda Allah Ya yi wa rasuwa ranar Juma'a.

Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya sanar da manema labaru cewa masu zaben Sarkin sun gabatar masa da wasu sunaye, wadanda a ciki ne zai zabi guda da ya amince da shi, domin nadawa a matsayin sabon Sarkin.

Daga cikin masu sha'awar mukamin akwai 'ya'yan marigayin, da kuma Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya.