Matasa Musulmi da Kirista ku zauna lafiya

Matasan Najeriya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Rikici tsakanin matasa Musulmai da Kirista na yawaita a dan tsakanin nan a kudancin jihar ta Kaduna.

A kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'ummun dake zaune a Kudancin jihar kaduna,wata kungiya mai zaman kanta mai suna Global Peace Foundation na shirya tarurrukan hadaka na musulmi da kirista matasa.

Kungiyar dai na kokarin wayar da kan matasan yankin musulmi da kirista ne a bisa amfanin zama lafiya duk da banbancin addini.

Kudancin jahar kaduna dai na fama da matsalolin rikice rikice masu nasaba da addini da kabilanci,duk da a baya musulmi da kirista na zaune lami lafiya.