Sanusi Lamido Sanusi ne Sarkin Kano

Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabon sarkin ya rike mukamin Dan majen Kano kafin ya zama Sarkin Kano

An ba da sanarwar nada tsohon gwamnan babban bankin Nigeria Mallam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Sarkin Kano.

Sakataren Gwamnatin Jahar Kano Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi shi ne ya bada sanarwar a madadin gwamnatin jahar Kano.

''Kamar yadda yake a bisa al'ada masu zabar masarautar sarki sun zauna sun tattauna sun baiwa gwamnati shawara akan wanda Allah Ya sa zai gaji marigayi Alhaji Ado Bayero.

Sakamakon haka gwamnati ta karbi shawarwarin su, kuma Allah Ya tabbatar wa Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, wanda zai gaji mai martaba Sarkin Kano a matsayin Sarkin Kano'' in ji Sakataren Gwamnatin Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi.

Mallam Sanusi Lamido Sanusi shi ne wanda ya gaji Marigayi Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu ranar juma'a bayan ya shafe fiye da shekaru 50 akan gadon sarauta.