Chibok: Dan majalisar Amurka ya je Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr. Smith dai ya ce zai kuma ziyarci birnin Rome domin tattaunawa kan fataucin 'yan matan Najeriya.

Wani dan majalisar wakillan Amurka ya kawo wata ziyara Najeriya domin duba batun fataucin yara da kuma tattara bayanai kan rawar da Amurka ke takawa wajen ceto 'yan matan nan na Chibok da ma halin da ake ciki na rikicin kungiyar Boko Haram.

Christopher Smith wanda shi ne shugaban kwamitin da kula da harkokin Afrika da kiwon lafiya da kare hakkin dan adam a majalisar ya ce 'yan Majalisar Amurkar za su sake zama kan batun Boko Haram ranar Laraba.

''Daya daga cikin dalilan da suka sa na zo nan shi ne batun fataucin 'yan mata. Ana fataucin 'yan mata da dama na Najeriya zuwa kasashen waje musamman zuwa birnin Rome; akwai kuma damuwa sosai kan 'yan matan nan na Chibok'' inji shi a cikin wata hira da BBC.

Sai dai ya ce ''Najeriya ce alhakin ceto 'yan matan Chibok ya rataya a wuyanta, amma kasashen duniya duniya na taka rawa sosai musamman ma ta bangaren tattara bayanan sirri da kuma bayar da horo.''

Karin bayani