An tarwatsa masu zanga-zanga a Brazil

Masu zanga zanga a Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A Brazil ne za'a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

'Yan sanda a birnin Sao Paulo na kasar Brazil sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga, mai alaka da yajin aikin da ma'aikatan jirgin karkashin kasa ke yi a kan neman karin albashi.

Tun da farko dai ma'aikatan sun kada kuri'ar ci gaba da kauracewa aikin nasu duk da cewa kotu ta hana su.

A birnin na Sao Paulo wanda shi ne birni mafi girma a Brazil za'a yi karawar farko a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za'a fara a wannan makon.

Gwamnan birnin Sao Paulo ya yi barazanar cewa zai kori ma'aikatan da suka ki komawa aiki.

Karin bayani