'Yan Nigeria na fama da matsala a Kamaru

'Yan Najeriya dake gudun Jamhuriyar  Kamaru Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Dubban 'yan Najeriya ne ke neman mafaka a Jamhuriyar Kamaru.

Rahotanni daga Jamhuriyar Kamaru sun ce dubban 'yan Najeriya da ke gudun hijira a kasar na fuskantar karancin muhalli.

Wannan matsala dai ta fi kamari a lardin arewa mai nisa na Kamaru da ke makwabtaka da wasu yankuna na arewacin Najeriya.

Dubban 'yan gudun hijira ne daga Najeriya ke neman mafaka a garuruwan Amchideda da Banga da Kuseri da kuma garin Fotokol na Jamhuriyar ta Kamaru.

Baya ga matsalar muhalli, 'yan gudun hijirar na fama da matsalar rashin lafiya, sakamakon raunuka da suka samu a lokacin da suka tserewa hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa a wasu sassa na Najeriya.

Karin bayani