Fyade: An cafke wasu maza bakwai a Masar

Wasu mata a alkahira lokacin rantsar da Al Sisi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai wasu na shakku game da batun

Ma'aikatar cikin gida ta Masar ta ce an cafke wasu maza bakwai bisa zargin yi wa wasu mata fyade, a lokacin shagulgulan kaddamar da Abdul Fattah Al Sisi.

Kamen ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna fushi game da wani faifan bidiyon da ke yawo a shafin intanet, wanda aka nuna wata mata tsirara.

Sannan aka yi wa matar fyade a tsakiyar wasu gungun maza.

Ana zargin lamarin ya faru ne a lokacin da ake shagulgulan rantsar da sabon shugaban kasar a dandalin Tahrir da ke Alkahira.

A makon jiya ne hukumomi a Masar a karon farko suka sanya dokar hana fyade, inda duk wanda aka samu da alaifi za a iya daure shi na tsawon shekaru biyar a kurkuku.