An rantsar da sabon Sarkin Kano

Image caption Gwamna Rabiu Kwankwaso da Sarki Sanusi Lamido Sanusi

An rantsar da sabon Sarkin Kano, Malam Sanusi Lamido Sanusi inda aka mika masa takardar shaidar kama aiki.

Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ya baiwa sabon Sarkin takardar kama aikin a gidan gwamnatin jihar Kano.

Wakilin BBC a Kano ya bayyana cewar kura ta lafa bayan an samu zanga-zangar adawa da kuma ta masu goyon bayan nadin tsohon shugaban babban bankin kasar, a matsayin Sarkin Kano.

Mai Martaba, Malam Sanusi Lamido Sanusi a jawabinsa ya ce rashin jituwar da aka samu babu hannun 'ya'yan gidan sarauta.

Ya ce "Na yi ammana babu wani dan gidan Sarauta da zai tunzura mutane su taka doka. Mu 'yan gida daya ne , kuma Allah ne ke bada mulki".

Wamban Kano, Alhaji Abbas Sanusi tare da sauran Hakimai sun yi wa sabon Sarkin mubaya'a.

Karin bayani