Mun kashe 'yan ta'adda 50 a Borno - Soji

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babban hafsan dakarun Nigeria, Air Marshal Alex Badeh

Dakarun tsaron Nigeria sun ce sun dakile wani hari a karshen mako a kan wasu kauyuka na jihohin Borno da Adamawa.

Sanarwar da rundunar tsaron ta fitar, ta ce dakarun sun kashe 'yan ta'adda fiye da hamsin sannan suka kwace makamai masu tarin yawa.

'Yan ta'addan a cewar sanarwar suna kan hanyarsu ta kai hare-hare ne a kan wasu kauyukan da ke kan hanyar Bilta a jihar Borno.

A cewar sanarwar, an raunata dakaru hudu lokacin ba ta kashin kuma a yanzu suna jinya a asibitin sojoji.

Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Boko Haram ke kaddamar da hare-hare a kauyukan jihar Borno inda suke hallaka mutane da dama.

Karin bayani