NUJ zata nemi diyya daga sojin Najeriya

Kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya, NUJ, ta ce zata nemi sojojin kasar da su biya 'ya'yanta diyya, saboda sun janyo masu cikas wajen gudanar da harkokinsu a 'yan kwanakin nan.

Sojojin dai sun hana rarraba jaridu a wuraren sayar da su saboda dalilan tsaro, kamar yadda suka ce.

Duk da cewa a yanzu an kawo karshen lamarin, kungiyar ta NUJ ta ce ya kamata sojojin su biya diyya saboda hasarar da suka janyo.

Shugaban kungiyar Malam Mohammed Garba, ya shaida BBC cewa zasu yi kiyasin irin asarar da sojojin sukayi masu kafun su san irin diyyar zasu nema daga wurin su.

A makon jiye ne sojoji a Najeriya suka hana raba sauran jaridu, saboda suna zargin cewa ana amfani da motocin raba jaridun wajen jigilar makamai.

Sojojin dai basu bada wata hujjar hakan ba, kuma lamarin ya janyo Allah wadai daga kungiyoyi dadama daga ciki da wajen kasar.