Sarki Sanusi: Kura ta lafa a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Kano a Nigeria na cewa al'amura sun lafa bayan an samu zanga-zangar adawa da kuma ta masu goyon bayan nadin tsohon shugaban babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi, a matsayin Sarkin Kano.

Sabon Sarkin ya yi wa manema labarai jawabi, inda ya yi alkawarin kare martabar jama'a da rayuka da kuma dukiyoyinsu.

Ya kuma musanta cewa an samu sabani a masarautar, yana mai cewa dukkansu daya ne.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka sanar da nadin Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi, wanda ya maye gurbin marigayi Sarki Ado Bayero.

Sai dai wadansu masana na kallon zanga-zangar adawar da ta goyon baya da cewa siyasa aka sanya a lamarin.