Sony ya shiga gaban Nintendo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sony da Nintendo da Microsoft suna hammaya

Sony ya shiga gaban Nintendo a karon farko cikin shekaru takwas, saboda yawan abubuwan wasannin bidiyo da kamfanin na Sony ya siyar.

Sony ya siyar da abubuwan wasan bidiyo guda miliyan 18.7 a cikin shekarar kudin da ta wuce har zuwa watan Maris, a yayinda shi kuma Nintendo ya sayar da kayayyakin wasan bidiyo miliyan 16.3.

Wani shafin kasuwanci na Japan ne ya soma bada wannan rahoton.

Labarin bai bada mamaki ba.

Wasan bidiyon PlayStation 4 na Sony ya kasance wasan bidiyon mafi farin jini inda ya shiga gaban Wii U da kamfanin Nintendo ya kera.

'Hamayya'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani na buga wasan bidiyon Nintendo

Sony da Nintendo da kuma Microsoft nan gaba za su fitar da sabobbin wasannin bidiyon da suka kera a wani bukin baje koli a Los Angeles.

Wannan rahoton na zuwa ne a daidai lokacin Nintendo ya sanarda rufe shalkwatarsa da ke Jamus.

Amma dai Nintendo na son ya fitar da Super Smash Bros 4 wanda ake ganin zai yi kasuwa sosai.

A cikin shekara guda, Nintendo ya tafka hasarar dala miliyan 229.

A nashi bangaren, Sony ya ce yana saran cewar PlayStation 4 ya kara yin kasuwa a cikin wannan shekarar.

Karin bayani