Al'ummar Gwoza sun kaurace wa gidajensu

Najeriya Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya Boko Haram

A Nigeria al'ummar yankin Gwoza da ke kudancin jihar Borno sun kaurace wa gidajensu saboda hare-haren da Boko Haram ke yawan kai musu.

Garin na Gwoza na daya daga cikin yankunan dake fama da tashe-tashen hankula da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Mazauna garin sun koka da cewa kwanaki tara kenan da suka bar gidajensu saboda farautar maza da 'yan kungiyar ke yi.

Matsalar rashin abinci da ruwan sha da sauran kayan more rayuwa na ci gaba da yin kamari.

Gwamnatin Najeriyar ta ce ta tura karin sojoji yankin, amma jama'ar sun ce har yanzu ba su ga komai ba.