Isra'ila na son zama 'yar kallo a Afirka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ministan wajen Isra'ila Avigdor Lieberman na ziyarar kwanaki goma a Afirka, domin neman Isra'ilar ta zama 'yar kallo a kungiyar tarayyar Afirka.

Mr. Lieberman ya fara wannan ziyara ce ranar Talata, inda zai je kasashen Ghana da Ivory Coast da Habasha da Kenya da Rwanda don inganta alakar tattalin arziki tsakanin kasashen da Isra'ila.

Ana sa ran yayin ziyararsa a Ghana, Mr. Lieberman zai gana da sarkin Ashanti, Otumfuo Nana Osei Tutu da mataimakin shugaban kasar, Kwesi Amissah-Arthur, sai Ministar wajen Ghana da takwaranta na tsaro.

Gabannin fara ziyarar, Mr. Lieberman ya ce dangantaka da kasashen Afirka abu ne mai matukar muhimmanci ga Isra'ila ta fuskar tsaro, diplomasiyya da tattalin arziki da sauran batutuwa da dama.