An harbe wani shehun malami a Kenya

Taswirar Kenya
Image caption Shi ne malami na hudu da aka kashe a Mombasa

Wasu 'yan bindiga sun harbe wani babban Malami, Sheikh Mohammed Idris a birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa da ke Kenya.

Sheikh Mohammed shi ne shugaban majalisar malamai masu wa'azi da kuma limamai na kasar.

'Yan bindigan sun harbe shi ne a kusa da wani masallaci da ba shi da nisa da gidansa.

Rahotanni sun ce a baya wasu matasa masu tsattsauran ra'ayi sun taba yi masa barazana, abin da ya sa ya ce rayuwarsa na cikin hadari.

Jami'an 'yan sanda a Mombasa sun bayyana cewar akwai takaddama game da shugabancin masallacin da Sheikh Muhammad yake Limanci.

Shi ne malamin addinnin Musulunci na hudu da aka kashe a Mombasa tun daga shekara ta 2012.

Karin bayani