'Yan gwagwarmaya masu Jihadi a Iraq na barazana a gabas ta tsakiya

Yan gwagwarmaya na ISIS a Iraqi
Image caption Yan gwagwarmaya na ISIS a Iraqi

Amurka ta yi kashedin cewa, kungiyar masu ikirarin yin jihadi dake fafutukar kafa daular musulunci a Iraqi da wasu kasashe makwabtanta, ta zama wata barazana bayan sun kwace iko da birnin Mosul, mai muhimmancin gaske a Iraqi.

Matasan birnin sun yi ta jifan motoci masu sulke na sojan gwamnatin Iraqi yayin da suke ficewa daga birnin bayan 'yan bindiga sun kore su daga cikinsa.

Wani da ya tsere daga birnin tare da iyalansa ya fadawa BBC cewa:

Ya ce, "yanzu dai dukkan birnin Mosul yana karkashin ikon masu kaifin kishin musuluncin, sun kai hari kuma sun kwace iko ga dukkan cibiyoyin tsaro na soja da 'yan sanda."

Rahotanni kuma na cewa 'yan bindigar sun kwace iko da wasu yankuna dake kusa da lardin Kirkuk.