Taron yaki da cin zarafin mata a duniya

Zainab Hawa Bangura
Image caption Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kan cin zarafin mata

Ministoci da masu fafutukar kare jinsi da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun jama'a sun fara isa birnin London domin halarta wani taro kan yaki da cin zarafin mata a duniya.

Ana sa ran mahalarta taron za su duba hanyoyin da za a bi don kawo karshen aikata laifin cin zarafin mata a duniya.

A wasu kasashen duniya ana samun matan da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata da su da kuma wasu nau'oin cin zarafi a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula.

Masu sharhi na ci gaba da tafka muhawara kan ko zaa ce ana ci gaba da aikata laifin cin zarafin mata duk kuwa da cewa ana daukar laifin cin zarafin mata a matsayin laifin yaki.