Masu kishin Islama sun kama Tikrit a Iraki

Dakarun ISIS Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun ISIS

Rahotanni daga Iraki na cewa, 'yan bindiga masu ikirarin yin jihadi sun kwace iko da birni na biyu a kasar cikin kwanaki biyu.

Wani rahoto ya ce, gungun mayakan kungiyar ta ISIS sun kwace iko da birnin Tikrit, wanda shi ne cibiyar mulkin lardin Salahuddin, kuma mahaifar Saddam Hussein.

Kungiyar ISIS din, wadda wani bangare ne na kungiyar Al Qaeda da ya balle, wadda kuma take yaki a Syria ma ta saki 'yan fursuna dama, lamarin da ake ganin zai kara karfafa karfinsu na yaki:

Nuri Al Maliki, Firaministan Irakin yana cewa, hakika ya yi imanin akwai wata makarkashiya a kwace iko da lardin Nineveh da 'yan kungiyar ISIS suka yi.