Wasu 'yan kasuwa a Jos sun shiga wani hali

Kasuwar Terminus Jos da aka taba kai harin bam Hakkin mallakar hoto
Image caption Kasuwar Terminus Jos da aka taba kai harin bam

Dubban 'yan-kasuwa a jihar Filaton Nijeriya sun ce sun shiga mawuyacin hali sanadiyar rashin sake bude kasuwarsu ta yankin Terminus.

Kasuwar ta yankin Terminus din dai nan ne inda aka samu tashin bama-bamai fiye da makonni ukku da suka gabata a birnin Jos.

Harin bama-baman daI sun hallaka jama'a da dama ne, da ya sa hukumomi suka killace yankin baki daya.

Amma a cewar 'yan kasuwar sun yi ta jira ko gwamnati za ta sake bude kasuwar amma har yanzu shiru kake ji, yayinda wasunsu ke kwana da yunwa.

To sai dai kuma gwamnatin ta bayyana cewa tana daukar wasu matakai ne na hana 'yan kasuwa dake harkokinsu a gefen titi sake komawa yankin saboda dalilai na tsaro.