Mata tsofaffi na karuwanci a Koriya

Image caption Zayyana a kan bango a wani titin Seoul babban birnin Koriya

Wasu mata tsofaffi 'yan kasar Koriya na shiga harkar karuwacin bayan da suka yanke kaunar cewa 'ya'yan da su ka haifa ba su da sukunin kulawa da su.

Galibin wadannan tsofaffin matan na fakewa ne da sayar da lemon kwalba mai kara kuzari da ake kira Bacchus wajen yin karuwanci.

Wata tsohuwa mai suna Kim Eun-ja mai shekaru 71 wacce ke sayar da lemon Bacchus ta ce, ba ta yi imanin cewa 'ya'yanta ba za su taimaka mata ba saboda halin da suka tsinci kansu a ciki.

Mrs Kim ta ce ta kan samu kusan dalar Amurka 3 ko 5 a kowace rana wajen sayar da lemon kwalba mai kara kuzari.

Sai dai ta ce bata shiga harkar karuwanci amma ta ce gilibi wasu matan kan fa ke ne da tallar Bacchus wajen yin karuwancin.

Rahotanni sun ce akasarin mata tsofaffi da ke karuwanci a kasar na haduwa kusa da wani wurin shakatawa na Jongmyo da ke tsakiyar birnin Seoul in da dattawa maza kan je domin su shakata.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An gina wannan wurin shakatawar ne a kusa da wurin bauta na Confucius wanda burin sa shine inganta rayuwar dattawa wanda kuma ya taimaka wajen habbaka al'adun kasar Koriya cikin shekaru da dama.

A wurin shakatawar, tsofaffin mata wadanda shekarun su ya kama daga 50, 60 har zuwa masu shekaru 70 kan tsaya a gefe inda su ke yi wa maza tallar lemon kwalba, kuma ta haka ne suke janyo ra'ayin mazajen har ta kai ga sun wuce da su zuwa Otel.

Tsofaffi a kasar Koriya ta kudu sun tsinci kansu a cikin wannan hali ne sakamakon yadda suka ta shi tsaye wajen bunkasa tattalin arzikin kasar su ta hanyar sadaukar da rayuwar su da kuma dan abun hannun su don samarwa wadanda ke tafe kyakyawar makoma.

Sai dai wannan yanayi ya sauya domin a yanzu matasa na cewa ba su da sukunin rike kansu da kuma iyayen su saboda sauyin da ake samu ta fuskar tattalin arziki.

Anata bangaren, gwamnati na fafutikar ganin ta samar da tsari na kyautata rayuwar al'umma, sai dai galibi tsofaffi maza da matan da ke taruwa a wurin shakatawa ta Jongmyo ba su tanadi komai ba kuma basu da fansho kuma ba su da 'yan uwan da za su dogara da su. A don haka ne su ka koma tamkar baki a kasar su ta haihuwa.

Wani masani mai suna Dr Lee Ho-Sun wanda ya gudanar da bincike akan wannan lamari, ya ce galibi tsofaffi matan da ke sayar da lemon kwalba mai kara kuzari na Bacchus sun shiga harkar karuwanci ne saboda halin talauci da suka shiga a lokacin da suka tsufa.