Ma'adanin Zinare a Hamadar Nijar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu masu hako zinare a jihar Nijar da ke Nigeria

Fiye da mutane dubu 10 ne suka yi wa tsaunukan Djado tsinke, inda aka gano wata babbar ma'adanar zinare cikin watan Afrilun da ya gabata a garin Bilma da ke kan iyakar Niger da Libya.

Shaidu da dama ne suka tabbatar da wannan lamari, don kuwa masu neman ma'adani, ba sa bukatar yin haka mai zurfi kafin su samu wannan dutse mai daraja, ga shi nan ma kawai a doron kasa.

Wani mai neman zinare, Mamane Sani ya ce abu ne mai muhimmanci ka samu na'urar gano zinare don samun kudi mai tarin yawa, a lokacin da yake sake godiya ga Allah da harshen Larabci.

Da irin wannan na'ura ce wani mai binciken zinare dan Nijeriya ya gano ma'adanin jibge a watan Afrilun da ya wuce cikin tsaunukan Djado da ke can kuryar arewacin Nijar kusa da Libya.

Magajin garin Djado, Sidy Lawal Abba ya fada wa BBC cewa kamar yadda aka saba, masu hakar ma'adanai da makiyaya ne da ke yawo neman ma'adani da ciyawa suka gano wannan waje.

Ya ce wajen neman sa'arsu, sai suka dace, ya nuna cewa ya zuwa yau, garin ya karbi bakuncin mutane dubu 13 da ababen hawa dubu 2 da 235.

'Yawon Bude Ido'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aikin hako zinare a kasar Colombia

A cewar wakilin BBC, sahara ba kawai shahara ta yi da abubuwan tashin hankali a yankin arewacin Nijar ba, don kuwa takan sanya annuri a fuskokin mutane bisa la'akari da wurin hakar zinaren da aka gano, a daya daga cikin yankuna masu fama da tsanani na kasar da ake kira Djado.

Bakin haure daga kasashe makwabta irinsu Nijeriya, Chadi, Libya da kuma Sudan na ta kwarara zuwa kasar.

Mai neman zinare dan kasar Chadi, Ousmane Ibrahim ya fada wa BBC cewa hukumomin Nijar ba su da wata matsala da 'yan kasashen waje da ke ci gaba da kwarara zuwa yanki, ya ce bako ba shi da shamaki a Nijar.

Takardu kawai yake bukata ya nuna ya tafi, ba tare da an karbi komai nasa ba.

Yawan masu hakar zinare a wannan lardi na sahara ya janyo karin tsadar rayuwa ciki har da hauhawar farashin kayan abinci.

Ruwa abokin rayuwa, ana sayar da duro mai cin lita 200 sama da CFA dubu 100 kusan dalar Amurka 200.

Ana safarar ruwan ne daga jihar Agadez, sauran masu hakar zinare kuma na samun ruwan daga wasu rijiyoyi kalilan da suka bijire wa fari a wadannan tsaunuka.

Karin bayani