Toyota zai janye motoci miliyan biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Prius na daga cikin samfarin motocin da aka janye

Katafaren Kamfanin kera motocin Toyota na Japan ya bukaci a janye motoci fiye da miliyan biyu saboda matsala a jakar iska mai rage tasiri hatsari.

An samu matsalar ce a samfurin motocin Toyota kimanin 20, ciki harda kirar Corolla Sedan da Toyota Yaris 'yar kumbula.

Matakin kari ne a kan janye motocin da kamfanin ya yi a bara.

Wani mai magana da yawun Toyota ya ce babu wanda ya jikkata ko ya samu hatsari sakamakon matsalar jakar iskar.

A cikin watan Afrilu ne Toyota ya kira a maida motoci kimanin miliyan shida da rabi don gyara matsalar da suke da ita ciki har da jakunkunan da iska da ba ta hura su idan an samu hatsari, da matsalar da ta shafi kujeru da sitiyari da makunnin motoci.

Karin bayani